Ƙidaya 11:4-9
4
Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana!
5
Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa.
6
Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!”
7
Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne.
8
Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun.
9
Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.
Settings