Nehemiya 7:1-2
1
Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa.
2
Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.