Nehemiya 4:8-12
8
Dukansu suka ƙulla su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su tā da hankali a cikinta.
9
Amma muka yi addu’a ga Allahnmu muka kuma sa masu tsaro da rana da kuma dare don mu magance wannan barazana.
10
Ana cikin haka, mutane a Yahuda suka ce, “Ƙarfin ma’aikata yana kāsawa, akwai kuma sauran tarkace da yawa da ba za mu iya sāke gina katangar ba.”
11
Abokan gābanmu sun ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”
12
Sau da yawa Yahudawan da suke da zama kusa da abokan gābanmu sun yi ta zuwa suna yin mana magana, suna cewa “Ko’ina muka juya, za su fāɗa mana.”
Settings