Skip to content
Nehemiya 13:19-21

Nehemiya 13:19-21

19
Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci.
20
Sau ɗaya ko biyu, ’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima.
21
Amma na ja kunnensu na ce, “Me ya sa kuke kwana kusa da katanga? In kuka ƙara yin haka, zan kama ku.” Daga wannan lokaci har zuwa gaba ba su ƙara zuwa a ranar Asabbaci ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options