Markus 9:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
2
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.
3
Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.
4
Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
Settings