Skip to content
Markus 6:35-38

Markus 6:35-38

35
A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure.
36
Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”
37
Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”
38
Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options