Markus 5:6-13
6
Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa.
7
Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”
8
Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”
9
Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”
10
Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin.
11
A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo.
12
Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.”
13
Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
Settings