Markus 5:15-20
15
Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro.
16
Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun.
17
Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu.
18
Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi.
19
Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”
20
Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
Settings