Malaki 3:13-18
13
“Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’
14
“Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki?
15
A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”
16
Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
17
“A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima.
18
Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
Settings