Skip to content
Malaki 1:11-14

Malaki 1:11-14

11
Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
12
“Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’
13
Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji.
14
“La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options