Luka 9:35-36
35
Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.”
36
Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan al’amari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.