Luka 20:34-38
34
Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
35
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.
36
Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.
37
Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
38
Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
Settings