Skip to content
Luka 11:1-4

Luka 11:1-4

1
Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”
2
Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.
3
Ka ba mu kowace rana abincin yini.
4
Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options