Skip to content
Firistoci 6:24-30

Firistoci 6:24-30

24
Ubangiji ya ce wa Musa,
25
“Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki.
26
Firist da ya miƙa ta zai ci, za a ci ta a tsattsarkan wuri, a harabar Tentin Sujada.
27
Duk abin da ya taɓa wani sashe na naman, zai zama da tsarki, kuma in wani jini ya ɗiga a riga, dole ka wanke shi a tsattsarkan wuri.
28
Dole a farfashe tukunyar lakar da aka dafa naman a ciki; amma in an dafa a tukunyar tagulla, sai a kankare tukunyar, a kuma ɗauraye da ruwa.
29
Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki.
30
Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options