Firistoci 26:42-45
42
zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.
43
Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina.
44
Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu.
45
Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”
Settings