Skip to content
Firistoci 26:19-29

Firistoci 26:19-29

19
Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla.
20
Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya.
21
“ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku.
22
Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku.
23
“ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni,
24
zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai.
25
Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba.
26
Sa’ad da na yanke abincinku, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, za su kuma rarraba abincin a ma’auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba.
27
“ ‘In duk da haka kuka ci gaba da ƙin saurare ni, kuka ci gaba da yin adawa da ni,
28
cikin fushina, sai in yi adawa da ku, in kuma hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai.
29
Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options