Firistoci 25:8-12
8
“ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.
9
Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku.
10
Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.
11
Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.
12
Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.
Settings