Firistoci 11:9-12
9
“ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.
10
Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.
11
Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.
12
Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.
Settings