Skip to content
Mahukunta 11:16-27

Mahukunta 11:16-27

16
Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh.
17
Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
18
“Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.
19
“Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’
20
Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila.
21
“Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar,
22
suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun.
23
“To, da yake Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya kori Amoriyawa a gaban mutanensa Isra’ila, wane ’yanci kake da shi da za ka karɓe ta?
24
Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi.
25
Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su?
26
Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon, Arower da ƙauyukan kewayenta da dukan biranen da suke gefen Arnon. Me ya sa ba ka karɓe su a lokacin ba?
27
Ban yi maka laifi ba, amma kana musguna mini ta wurin kawo mini hari. Bari Ubangiji yă zama Alƙali, yă yanke hukunci tsakani Isra’ilawa da Ammonawa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options