Mahukunta 11:13-22
13
Sarkin Ammonawa ya ce wa jakadu, “Sa’ad da Isra’ilawa suka fito daga Masar, sun ƙwace mini ƙasa tun daga Arnon zuwa Yabbok, har zuwa Urdun. Yanzu ka mayar mini ita cikin salama.”
14
Yefta ya sāke aikan jakadu wurin sarki,
15
yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.
16
Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh.
17
Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
18
“Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.
19
“Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’
20
Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila.
21
“Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar,
22
suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun.
Settings