Yunana 1:4-10
4
Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.
5
Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa.
6
Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.”
7
Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana.
8
Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?”
9
Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”
10
Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)
Settings