Ayuba 42:12-16
12
Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.
13
Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku.
14
’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk.
15
Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.
16
Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.
Settings