Skip to content
Irmiya 36:9

Irmiya 36:9

Ana nuna aya 9 tare da mahallin da ke kewaye.
6
Saboda haka ka tafi gidan Ubangiji a ranar azumi ka karanta wa mutane daga littafin maganar Ubangiji da na shibta maka ka rubuta. Ka karanta su ga dukan mutanen Yahuda waɗanda suka zo daga garuruwansu.
7
Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.”
8
Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya ce ya yi; a haikalin Ubangiji kuwa ya karanta maganar Ubangiji daga littafin
9
A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda.
10
Daga ɗakin Gemariya ɗan Shafan magatakarda, wanda yake a fili na bisa a mashigin Sabuwar Ƙofar haikali, Baruk ya karanta wa dukan mutane a haikalin Ubangiji maganar Irmiya daga littafin.
11
Sa’ad da Mikahiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji daga littafin,
12
sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options