Irmiya 18:1-6
1
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
2
“Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”
3
Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.
4
Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
5
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
6
“Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.
Settings