Irmiya 16:13-18
13
Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’
14
“Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’
15
amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.
16
“Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu.
17
Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba.
18
Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.”
Settings