Irmiya 13:6-10
6
Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.”
7
Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam.
8
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima.
10
Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!
Settings