Irmiya 12:1-4
1
Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?
2
Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu.
3
Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka!
4
Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya ciyawar kowane fili ta bushe? Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne, dabbobi da tsuntsaye sun hallaka. Ban da haka ma, mutane suna cewa, “Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”
Settings