Lompat ke konten
Irmiya 10:3-9

Irmiya 10:3-9

3
Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.
4
Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi.
5
Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.”
6
Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko.
7
Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka.
8
Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu.
9
An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options