Yaƙub 2:14-17
14
Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?
15
A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,
16
sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?
17
Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings