Yaƙub 1:13-18
13
Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;
14
amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.
15
Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.
16
Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu.
17
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
18
Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.
Settings