Ishaya 58:7-12
7
Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
8
Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.
9
Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,
10
in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.
11
Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
12
Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
Settings