Ishaya 58:11-14
11
Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
12
Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
13
“In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki, in kuka kira Asabbaci ranar murna rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma, in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu,
14
sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa.
Settings