Ishaya 55:6-9
6
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.
7
Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.
8
“Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji.
9
“Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa tunanina kuma dabam da naku.
Settings