Ishaya 5:11-17
11
Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi.
12
Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
13
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
14
Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.
15
Ta haka za a ƙasƙantar da mutum kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam, za a ƙasƙanta da masu girman kai.
16
Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya, kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
17
Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu; raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.
Settings