Skip to content
Ishaya 47:8-11

Ishaya 47:8-11

8
“To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’
9
Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.
10
Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
11
Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options