Ishaya 43:8-11
8
Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi, waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame.
9
Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”
10
“Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba.
11
Ni kaɗai, ni ne Ubangiji, kuma in ban da ni babu wani mai ceto.
Settings