Aller au contenu
Ishaya 41:26-29

Ishaya 41:26-29

26
Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.
27
Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi.
28
Na duba amma ba kowa ba wani a cikinsu da zai ba da shawara, ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su.
29
Duba, dukansu masu ƙarya ne! Ayyukansu ba su da riba; siffofinsu iska ne kawai da ruɗami.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options