Ishaya 20:3-6
3
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,
4
haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.
5
Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.
6
A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”
Settings