Skip to content

Ishaya20

1
A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi,
2
a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.
3
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,
4
haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.
5
Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.
6
A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options