Skip to content
Ishaya 12:1-3

Ishaya 12:1-3

1
A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.
2
Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”
3
Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options