Skip to content
Ishaya 1:12-18

Ishaya 1:12-18

12
Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?
13
Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
14
Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.
15
Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!
16
Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.
17
Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.
18
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options