8
“Efraim yana cuɗanya da al’ummai; Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.
9
Baƙi sun tsotse ƙarfinsa, amma bai gane ba. Gashi kansa ya cika da furfura, amma bai lura ba.
10
Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa, amma duk da haka bai dawo ga Ubangiji Allahnsa ko yă neme shi ba.