Ibraniyawa 9:12-14
12
Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.
13
In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
14
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
Settings