Ibraniyawa 9:11-15
11
Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.
12
Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.
13
In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
14
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
15
Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.
Settings