Skip to content
Ibraniyawa 8:1-6

Ibraniyawa 8:1-6

1
Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama,
2
wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
3
Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa.
4
Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye.
5
Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
6
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options