Skip to content
Ibraniyawa 7:21-25

Ibraniyawa 7:21-25

21
shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”
22
Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
23
To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist;
24
amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada.
25
Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options