Ibraniyawa 6:13-15
13
Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,
14
cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”
15
Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.