Ibraniyawa 10:11-18
11
Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.
12
Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.
13
Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa,
14
gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.
15
Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce,
16
“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”
17
Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.”
18
In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.
Settings