Skip to content
Haggai 2:3-9

Haggai 2:3-9

3
‘Wane ne a cikinku ya ragu da ya ga wannan gida a darajarsa ta dā? Yaya yake a gare ku a yanzu? Bai yi kamar a bakin kome ba, ko ba haka ba?
4
Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
5
‘Wannan shi ne alkawarin da na yi da ku a lokacin da kuka fito daga Masar. Ruhuna kuwa yana tare da ku. Kada ku ji tsoro.’
6
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa.
7
Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
8
‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
9
‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options