Haggai 2:11-12
11
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku tambayi firist abin da doka ta ce.
12
Idan mutum yana riƙe da naman da aka keɓe a rigarsa, sa’an nan kuma wannan rigar ta taɓa burodi, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin yă zama tsarkake?’ ” Firistoci suka amsa, suka ce, “A’a.”
Settings